7. Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’
8. “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.
9. “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”
10. (Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā.
11. Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa.
12. Haka nan kuma a dā Horiyawa ne suke zaune a ƙasar Seyir, amma mutanen zuriyar Isuwa suka zo, suka kore su, suka karkashe su, suka zauna a wurin, daidai kamar yadda Isra'ilawa suka yi da ƙasar mallakarsu, wadda Ubangiji ya ba su.)