M. Sh 2:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir.

2. “Sai Ubangiji ya ce mini.

3. ‘Ai, kun daɗe kuna ta gewaya waɗannan tuddai. Ku juya, ku nufi arewa.

4. Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali,

5. kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.

6. Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu.

7. Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’

8. “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.

9. “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”

10. (Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā.

M. Sh 2