6. don kada mai bin hakkin jini ya bi shi da zafin fushinsa, ya cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da ya ke ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā.
7. Domin haka na umarce ku, ku keɓe wa kanku garuruwa uku.
8. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta wa kakanninku, har ya ba ku dukan ƙasar da ya alkawarta zai ba kakanninku,
9. in dai kun lura, kun kiyaye umarnin da nake umartarku da shi yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa kullum, sa'an nan sai ku ƙara garuruwa uku a kan waɗannan uku ɗin kuma,
10. don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.
11. “Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa'an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan,
12. sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa'an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi.
13. Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya.
14. “A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”