M. Sh 14:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya,

5. da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse.

6. Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa.

7. Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.

M. Sh 14