27. “Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku.
28. A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku.
29. Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”