11. sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.
12. Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku.
13. Ku lura, kada ku miƙa hadayunku na ƙonawa ko'ina,
14. amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.
15. “Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar sarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri.
16. Amma ba za ku ci jinin ba, sai ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
17. Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.
18. Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi.
19. Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.
20. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa'an nan ku ce, ‘Ina so in ci nama,’ saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so.