1. “Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.
2. Sai ku hallaka dukan wuraren da al'umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu.
3. Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.
4. “Ba haka za ku yi wa Ubangiji Allahnku ba.
5. Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.
6. A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.