M. Sh 1:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’

18. A wancan lokaci na umarce ku da dukan abin da ya kamata ku yi.”

19. “Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.

20. Sa'an nan na faɗa muku cewa, ‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.

21. Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’

22. “Sa'an nan sai dukanku kuka zo wurina, kuka ce, ‘Bari mu aika da mutane, su je su leƙo mana asirin ƙasar tukuna, domin su shawarce mu ta hanyar da za mu bi, da kuma irin biranen da za mu shiga.’

23. “Na ga al'amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila.

24. Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.

M. Sh 1