1. Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.
2. Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.
3. A shekara ta arba'in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra'ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu.
4. A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai.
5. A hayin Urdun, cikin ƙasar Mowab, Musa ya yi niyya ya fassara waɗannan dokoki.Ya ce,
6. “Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.
7. Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan'aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis.
8. Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”
9. “A wancan lokaci ne na yi magana, na ce, ‘Ba zan iya ɗaukar nawayarku ba,
10. gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.