M. Had 2:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na sa rai in ji wa kaina daɗi, in kuma san yadda farin ciki yake. Sai na tarar wannan ma aikin banza ne.

2. Na kuma gane dariya wauta ce, nishaɗi kuma ba shi da wani amfani.

3. Muradina shi ne in san hikima in nemi yadda zan ji wa raina daɗi da ruwan inabi, in sa kaina ga aikata wawanci. Bisa ga tsammanina mai yiwuwa ne wannan shi ne abu mafi kyau da mutane za su yi a duniya, a 'yan kwanakinsu.

4. Na kammala manyan abubuwa. Na gina wa kaina gidaje, na yi gonakin inabi.

5. Na kuma yi wa kaina lambuna da gonakin itatuwa, ba irin itatuwa masu 'ya'ya da ba su a ciki.

M. Had 2