M. Had 12:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kalmomin mutane masu hikima kamar sanduna suke da makiyaya suke amfani da su, su bi da tumaki.

12. Ya ɗana, ka yi hankali, kada ka zarce waɗannan, gama wallafa littattafai ba shi da iyaka, yawan karatu kuma gajiyar da kai ne!

13. Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum.

14. Allah zai shara'anta kowane irin aiki, ko a ɓoye aka yi shi, ko nagari ne, ko mugu.

M. Had 12