Luk 7:48-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

48. Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

49. Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?”

50. Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”

Luk 7