Luk 7:39-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”

40. Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.”

41. Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.

42. Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?”

43. Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.”

44. Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta.

45. Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba.

46. Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna.

47. Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.”

48. Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

Luk 7