16. da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.
17. Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu.
18. Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.