Luk 24:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.

5. Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu?

6. Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili

7. cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.”

8. Sai suka tuna da maganarsa.

9. Da suka dawo daga kabarin suka shaida wa goma sha ɗayan nan, da kuma duk sauransu, dukan waɗannan abubuwa.

10. To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa.

Luk 24