Luk 24:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala'ikun da suka ce yana da rai.

24. Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”

25. Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!

26. Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?”

27. Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.

28. Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba,

29. suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu.

30. Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.

31. Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu.

32. Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa'ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”

33. Anan take, suka tashi suka koma Urushalima, suka sami sha ɗayan nan tare gu ɗaya, da kuma waɗanda suke tare da su,

34. suna cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!”

35. Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi a wajen gutsura gurasa.

36. Suna cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama alaikun!”

Luk 24