Luk 24:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Suna ta zance da juna a kan dukan al'amuran da suka faru.

15. Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare.

16. Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba.

Luk 24