36. Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,
37. suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”
38. Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”
39. Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!”
40. Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa?
41. Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.”
42. Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.”
43. Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”
44. To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
45. Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu.
46. Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.
47. Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”
48. Sa'ad da duk taro masu yawa, waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, suka koma, suna bugun ƙirjinsu.
49. Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.
50. To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma.
51. Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah.
52. Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
53. Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba.