1. Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
2. Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”
3. Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.”
4. Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.”