Luk 21:35-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.

36. Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

37. Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.

38. Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

Luk 21