Luk 20:40-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

41. Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

42. Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a damana,

43. Sai na sa ka take maƙiyanka.” ’

Luk 20