22. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?”
23. Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu,
24. “Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”
25. Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
26. Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.