Luk 18:40-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi,

41. “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!”

42. Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

43. Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

Luk 18