1. Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu!
2. Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.
3. Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.