46. ai, ubangijin wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana.
47. Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka,
48. Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”
49. “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!
50. Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!
51. Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa.
52. Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku.