28. To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!
29. Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini.
30. Ai, al'umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.
31. Ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.
32. “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.
33. Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,
34. don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”
35. “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne.
36. Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa.