Luk 11:52-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

52. Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”

53. Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa,

54. suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.

Luk 11