Luk 11:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana,

6. ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,’

7. sa'an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, ‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da 'ya'yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’

8. Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.

9. Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

10. Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

11. Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji?

12. Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?

13. To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

14. Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.

15. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

16. Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.

Luk 11