Luk 1:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa'ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,

9. bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

10. A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a,

Luk 1