Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina.