Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?”