L. Mah 17:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika.

2. Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.”Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”

L. Mah 17