L. Mah 15:19-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.

20. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

L. Mah 15