L. Mah 1:33-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan'aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu.

34. Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba.

35. Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu.

36. Iyakar Amoriyawa ta nausa ta kan hawan Akrabbim daga Sela zuwa gaba.

L. Mah 1