1. Ubangiji ya ba Musa
2. waɗannan umarnai domin jama'ar Isra'ila. Sa'ad da suka shiga ƙasar Kan'ana ga yadda iyakokin ƙasashensu za su zama.
3. Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas.
4. Sa'an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa'an nan ta miƙa zuwa Hazar'addar, ta zarce ta bi ta Azemon.
5. Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar.
6. Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.
7. Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor.
8. Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.
9. Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.