18. Da suka tashi daga Hazerot, sai suka sauka a Ritma.
19. Suka tashi daga Ritma suka sauka a Rimmon-farez.
20. Suka tashi daga Rimmon-farez, suka sauka a Libna.
21. Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa.
22. Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata.
23. Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer.
24. Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada.