5. Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra'ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.
6. Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele'azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.
7. Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8. Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.