L. Kid 31:39-53 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500), daga ciki aka fitar da jakai sittin da ɗaya domin Ubangiji.

40. 'Yan mata dubu goma sha shida (16,000), daga ciki aka fitar da 'yan mata talatin da biyu domin Ubangiji.

41. Sai Musa ya ba Ele'azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

42. Wannan shi ne kashin da aka ba jama'ar Isra'ila cikin kashin da aka ware daga na waɗanda suka tafi yaƙin.

43. Tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari bayar (337,500),

44. shanu dubu talatin da dubu shida (36,000),

45. jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500),

46. 'yan mata dubu goma sha shida (16,000).

47. Daga rabin kashi na jama'ar Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na 'yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

48. Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa.

49. Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu.

50. Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da 'yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”

51. Musa da Ele'azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka.

52. Dukan zinariya da shugabanni suka bayar hadaya ga Ubangiji, nauyinta ya kai shekel dubu goma sha shida da ɗari bakwai da hamsin (16,750).

53. Kowane soja ya kwashi ganimarsa.

L. Kid 31