L. Kid 26:30-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. 'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,

31. da Asriyel, da Shekem,

32. da Shemida, da Hefer.

33. Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

34. Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).

35. Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat.

36. Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne.

37. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500).

38. Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram,

39. da Shuffim, da Huffim.

40. Iyalin Adar da na Na'aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne.

41. Waɗannan su ne 'ya'yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari shida (45,600).

42. Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan.

43. Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).

L. Kid 26