L. Kid 26:28-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.

29. Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad.

30. 'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,

31. da Asriyel, da Shekem,

32. da Shemida, da Hefer.

33. Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

L. Kid 26