13. da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.
14. Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200).
15. Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni,
16. da Ezbon, da Eri,
17. da Arodi, da Areli.
18. Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500).
19. Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana).
20. Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,
21. da Hesruna, da Hamul.
22. Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500).