19. Yakubu zai yi mulki,Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”
20. Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Amalek na fari ne cikin al'ummai,amm ƙarshensa hallaka ne.”
21. Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Wurin zamanku mai ƙarƙo ne,Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.
22. Duk da haka za a lalatar da Keniyawa.Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?”
23. Sai kuma ya hurta jawabinsa, ya ce,“Kaito, wa zai rayu sa'ad da Allah ya yi wannan?