45. “Ku nisanci wannan taro, gama yanzun nan zan hallaka su.”Sai suka fāɗi rubda ciki.
46. Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki farantin turare, ka cika shi da wuta daga bagade, ka zuba turaren wuta a ciki, ka tafi da sauri wurin taron, ka yi kafara dominsu, gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko, an fara annoba.”
47. Sai Haruna ya ɗauko farantin turaren, ya yi yadda Musa ya ce. Ya sheƙa a guje a tsakiyar taron jama'a. Amma an riga an fara annobar a cikin jama'a. Sai ya zuba turare, ya yi kafara domin jama'a.
48. Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.
49. Waɗanda annoba ta kashe mutum dubu goma sha huɗu ne da ɗari bakwai (14,700), banda waɗanda suka mutu a sanadin Kora.
50. Sai Haruna ya koma wurin Musa a ƙofar alfarwa ta sujada, gama annobar ta ƙare.