11. Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.
12. Zai kai wa firist garin, firist zai ɗibi garin cike da tafin hannunsa, wannan shi ne kashi na tunawa. Zai ƙone shi bisa bagaden kamar hadaya na ƙonawa ga Ubangiji, gama hadaya ce don laifi.
13. Ta haka firist zai yi kafara don laifin da mutumin ya aikata daga cikin abubuwan nan, za a kuwa gafarta masa. Sauran garin zai zama na firist kamar yadda yakan zama nasa a hadaya ta gari.