L. Fir 26:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.

10. Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo.

11. Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.

L. Fir 26