19. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla.
20. Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.
21. “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.
22. Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.
23. “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
24. sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.
25. Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.
26. Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.
27. “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
28. sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.
29. Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.