L. Fir 18:17-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.

18. Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.

19. Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki.

20. Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa.

L. Fir 18