L. Fir 18:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce.

14. Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce.

15. Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.

16. Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce.

17. In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.

18. Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.

19. Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki.

20. Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa.

21. Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne.

22. Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan.

23. Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu.

24. Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu.

L. Fir 18