L. Fir 18:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2. ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku.

3. Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu.

4. Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

L. Fir 18