5. Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.
6. Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
7. Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.
8. Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka,
9. amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.